Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta yi gargadi game da tasirin COVID-19 kan zaman lafiya da tsaro
2020-07-03 10:41:38        cri

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya tunatar da kwamitin sulhu na MDD game da munanan tasirin COVID -19 kan zaman lafiya da tsaro a duniya.

Antonio Guteress, ya ce ana iya ganin illolinta a wasu kasashen da ake ganin na da zaman lafiya. Amma tasirinta ya fi bayyana a kasashen da suke fuskantar rikici ko kuma suke farfadowa daga rikici, da kuma wadanda ka iya tsundunma ciki nan ba da dadewa ba.

Ya kara da cewa, ana kara shiga fargaba saboda matsananciyar matsalar tattalin arziki. Sannan amincin da ake da shi kan cibiyoyin gwamnati na raguwa a wuraren da ake ganin hukumomi ba su dauki matakan da suka dace na yaki da cutar ba, ko kuma ba su bayyana ainihin tasirinta ba.

Ya kara da cewa, annobar na ta'azzara matsalar wariyar jinsi, bisa la'akari da yadda mata suka fi yawa a fannonin da ta fi shafa. Baya ga haka, akwai karuwar cin zarafinsu, da kuma gazawar wadanda aka ci zarafi na kai kara da neman mafaka da kuma bi musu hakki. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China