Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tawagogi 15 masu binciken riga kafin COVID-19 a fadin duniya sun gabatar da tsarukan gwaji
2020-07-03 13:09:09        cri

Tawagogi 15 masu binciken riga kafin COVID-19 a fadin duniya, da suka shiga matakin fara gwaji kan mutane, sun gabatar da tsarukansu na gwaji, yayin taro na 2 kan bincike da samar da riga kafi da aka kammala a jiya.

Babbar masaniyar kimiyya ta hukumar lafiya ta duniya WHO Soumya Swaminathan ce ta bayyana haka yayin wani taron manema labarai a jiya.

Soumya Swaminathan, ta ce taron ya gudana ne daga ranar 1 zuwa 2 ga wata, inda masana kusan 1,300 daga kasashe da yankuna 93 suka halarta. Ta ce dukkan masana kimiyyar sun nuna kudurinsu na hada hannu da tattaunawa mai zurfi game da bincike na gaba da dabarun jinya da riga kafi.

A nata bangaren, shugabar sashen bincike da samar da riga kafi na WHO, Ana Maria Henao Restrepo, ta ce sama da riga kafin COVID-19 150 ake kokarin samarwa a duniya, kuma za a samu wasu kari da za su shiga matakin gwaji kan bil adama. Ta kara da cewa, ba zai yiwu a ba da jadawalin lokacin da za a fara amfani da riga kafin ba, amma abu mai muhimmanci shi ne, an cimma matsaya tare da hada hannu kan batutuwa da dama. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China