Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta harba tauraron dan-Adam dake iya dauko hotuna masu inganci
2020-07-03 13:33:26        cri

Hukumar kula da harkokin sararin samaniyar kasar Sin, ta sanar a yau Jumma' cewa, kasar ta yi nasarar harba wani tauraron dan-Adam dake iya daukar hotuna masu inganci cikin sararin samaniya daga cibiyar harba taurarin dan-Adam ta Taiyuan dake lardin Shanxi a yankin arewacin kasar.

An dai harba tauraron ne ta hanyar amfani da rokar Long March-4B da misalin karfe 11 da mintuna 10 na safiyar yau agogon birnin Beijing na kasar Sin.

Wannan shi ne na karo na 337, da aka yi amfani da rokar Long March wajen harba taurarin dan-Adam. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China