Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Labarin kawar da talauci na magatakardan reshen jam'iyyar JKS na kauyen Tuanjie
2020-07-03 14:57:13        cri
Bayan ya kammala karatunsa a jami'ar Guizhou, Hu Junpu ya kama aiki a matsayin magatakardan reshen jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, a kauyen Tuanjie na garin Shimen dake yankin Weining mai cin gashin kansa na kabilun Yi da Hui da Miao a lardin Guizhou na kasar Sin. Ya ce, a lokacin da yake karatu a jami'a, galibin abokan karatunsa sun yi fatan yin ayyuka a manyan birane kamar birnin Beijing, ko birnin Shanghai ko kuma birnin Guangzhou, amma a ganinsa, yin aiki a kauyuka, wata kyakkyawar dama ce, shi ya sa, da ya kammala karatunsa a jami'a, ya kama aiki a kauyen Tuanjie.

Amma a lokacin farko da ya isa kauyen Tuanjie a shekarar 2016, yanayin da kauyen yake ciki ya bakanta masa rai sosai. Wannan kauyen dake cikin tsaunuka yana fama da talauci mai tsanani, har adadin masu fama da talauci da ya kai 48% a lokacin.

Sa'an nan, bayan binciken da ya yi, ya shigar da irin tafarnuwa dake iya jure sanyi daga garin Zhongshui dake makwabtaka da kauyen. Ya zuwa yanzu, an shuka irin wannan tafarnuwa har fadinsu ya kai sama da muraba'in mita dubu 133 a kauyen Tuanjie, kuma ana iya samar da tafarnuwa sama da kilogiram 500 cikin fadin gona mai muraba'in mita 667, kana, ana sayar da tafarnuwa na kilogiram 0.5 kan yuan shida, lamarin da ya kara kudin shiga ga al'ummomin kauyen.

Ya zuwa karshen shekarar 2019, aka kawar da talauci baki daya a kauyen Tuanjie.

Cikin wadannan shekaru uku da rabi, Hu Junpu ya karu sosai, kuma, zuciyarsa ta cika da fata.

Kuma, abin da ya fi burge shi shi ne, bi da bi, ya cika dukkanin fatan da ya yi wa kauyen Tuanjie. Ya ce, ya zo kauyen Tuanjie domin kiran da JKS ta yi masa, kuma kawar da talauci a kauyen ya zama nauyin dake wuyansa a matsayin mamban JKS, tabbas, zai warware dukkanin matsalolin dake gabansa cikin hadin gwiwa da al'ummomin kauyen, da cimma burin gina zaman takewar al'umma mai wadata. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China