Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hadin kai da tattaunawa tare don inganta ayyukan kare hakkin bil Adama
2020-07-03 17:00:28        cri

 

A cikin shekaru 75 da suka gabata, an fuskanci kalubale wajen inganta harkokin kiyaye hakkin bil Adama a duniya. Har zuwa yanzu, yadda za a gudanar da wannan aikin ya kasance wata babbar matsala dake damun kasashe daban daban.

Sakamakon yaduwar annobar COVID-19 ta shafi yawancin tarukan MDD, amma duk da haka an bude taron hukumar hakkin bil Adama ta MDD karo na 44 a ranar 30 ga watan Yuni a Geneva kamar yadda aka tsara.

Hukumar kare hakkin bil Adama ita ce ta maye gurbin kwamitin kare hakkin bil Adama na majalisar. Bisa tsarin kwamitin, kullum kasashen yamma suna ta matsin lamba da nuna kiyayya a fannin siyasa ga kasashe masu tasowa, don haka, aka yiwa tsarin hakkin bil Adama na majalisar kwaskwarima. A shekarar 2006, a yayin babban taron MDD, an tsaida kudurin soke kwamitin kare hakkin bil Adama, inda aka kafa hukumar kare hakkin bil Adama.

 

 

Kasar Amurka wadda ko da yaushe ke magana kan demokuradiyya da hakkin bil Adama, ta yi watsi da ci gaba mai yakini da aka samu kan gyare-gyaren da MDD ke yi, har ma ta fice daga zaben kasashe mambobi dake da alhakin kafa hukumar hakkin bil Adama. A lokacin gwamnatin Barack Obama, kasar Amurka ta nemi shiga hukumar, amma a lokacin gwamnatin Donald Trump wadda ke nuna ra'ayin rashin adalci da gaskiya, kasar ta fice daga hukumar. Lallai, kasar Amurka na yin kome ne bisa burin da ita kanta kadai take son cimmawa.

A nata bangare, kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan manufar zaman daidai wa daida da girmama juna tsakanin kasashe daban daban, da tsarin dokoki da ka'idojin alakar kasa da kasa, don gudanar da tattaunawa mai yakini. A ganinta, ya kamata a cimma nasara tare ta hanyar hadin kai, da inganta gudanar da harkokin kare hakkin bil Adama tare, da kuma gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adam. Yadda hukumar hakkin bil Adama ke iya gudanar da ayyukanta da taka rawarta yadda ya kamata, wannan ya dogaro da shawarar kasancewar bangarori da dama, da nuna amincewa da juna da sada zumunci da yin hadin kai da tattaunawa a tsakanin gwamnatoci da al'ummomin kasashe daban daban.

Yanzu kasashen duniya na kara kulla alaka a tsakaninsu, wannan shi ne dalilin karfafa hadin gwiwa a tsakanin bil Adama, musamman ma a fannin tinkarar wasu wahalhalu da hadurra yayin da ake kokarin dunkulewar tattalin arzikin duniya. Bai kamata ba wata kasa ta kawo cikas ga hadin kan kasa da kasa bisa ra'ayinta na yakin cacar baki da babakere. (Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China