Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashe fiye da 70 sun nuna goyon baya ga kasar Sin kan kafuwar dokar tsaron kasa mai nasaba da Hong Kong
2020-07-03 19:41:36        cri
Bayan da wasu kasashe 53 suka bayyana farin cikinsu, na ganin majalissar wakilan jama'ar kasar Sin ta zartas da dokar tsaron kasa mai nasaba da yankin Hong Kong na kasar, karin wasu kasashen fiye da 20, su ma sun nuna gayon baya ga kasar Sin dangane da wannan batu, A ranar 1 da 2 ga watan da muke ciki. Karin kasashen sun bayyana hakan ne a gefen taron kwamitin hakkin dan Adam na MDD.

Cikin wadannan kasashe, Burundi ta yabawa kasar Sin, game da kokarinta a fannin kare hakkin dan Adam, da gudunmowar da kasar ta Sin ta samar ta fuskar kare hakkin bil Adama a duniya. A cewar kasar, kafuwar dokar tsaron kasa mai nasaba da yankin Hong Kong, za ta taimaka wajen kare hakkin dan Adam a yankin.

A nata bangaren, kasar Kamaru ta nuna kin amincewa da yadda wasu kasashe suke amfani da batun Hong Kong, da na Xinjiang, wajen tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Sin.

Sa'an nan kasashen da suka hada da Najeriya, da Aljeriya, da Morocco, sun bayyana cewa, ya kamata a girmama wasu manyan ka'idojin da ake bi wajen kula da huldar kasa da kasa, maimakon fakewa da batun hakkin dan Adam, don neman yin shisshigi cikin harkokin gidan wata kasa. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China