Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kakakin Sin: Dokar tsaron kasar mai nasaba da Hong Kong za ta amfani masu zuba jari
2020-07-03 19:45:58        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, mista Zhao Lijian, ya furta a yau Jumma'a cewa, kafuwar dokar tsaron kasa mai nasaba da yankin Hong Kong, da yadda ake aiwatar da ita, za su taimakawa kokarin tabbatar da hakki na masu zuba jari na kasashe daban daban. Sa'an nan yana sa ran ganin kamfanoni masu jarin waje dake yankin Hong Kong, sun samu makoma mai haske a nan gaba

Kafin hakan, kungiyar 'yan kasuwan kasar Amurka dake yankin Hong Kong, ta fitar da wata sanarwa, inda ta ce cikin shekaru fiye da 50 da suka wuce, kungiyar ta yi kokarin kare matsayin yankin Hong Kong, na wata cibiyar kasuwanci ta kasa da kasa. Kana har zuwa yanzu, wannan ra'ayi na ta dangane da yankin na Hong Kong bai taba canzawa ba. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China