Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta ja hankalin wasu kasashe da su dakatar da fakewa da 'yancin bil Adama suna tsoma baki cikin harkokin gidan wasu
2020-07-03 20:12:03        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce kasarsa na fatan wasu kasashe za su dakatar da fakewa da 'yancin bil Adama, suna tsoma baki cikin harkokin gidan wasu kasashen na daban.

Zhao ya ce Sin na fatan irin wadannan kasashe za su gyara kurakuransu game da batun hakkin bil Adama, su daina siyasantar da wannan batu, tare da daukar matsaya biyu.

Jami'in ya kara da cewa, batun jihar Xinjiang yana da alaka ne da yaki da ta'addanci, da kawar da tsattsauran ra'ayi, ba wai batun wata kabila, addini da hakkin bil Adama ba, kuma gwamnatin Sin na aiwatar da matakai daban daban a yankin bisa tanajin doka.

Daga nan sai Mr. Zhao ya jaddada adawar Sin ga kasashen da ke fakewa da 'yancin dan Adam, a matsayin hujjar tsoma baki cikin harkokin gidan sauran kasashe. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China