Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bugawa takwaransa na Malawi waya don taya shi murna
2020-07-03 20:17:57        cri

A yau Juma'a ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bugawa takwaransa na kasar Malawi Lazarus Chakwera waya, don taya shi murnar darewa karagar shugabancin kasarsa.

Yayin zantawar tasu, shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, a cikin shekaru 13 da kafuwar dangantakar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu, an kara amincewa da juna a siyasance, da kuma samun ci gaba mai armashi, a fannin hadin kai tsakanin kasashen biyu. Kaza lika Sin ta dora babban muhimmanci kan bunkasuwar dangantakar kasashen biyu, kuma shugaba Xi yana mai fatan kara hadin kai da Lazarus Chakwera, don ingiza hadin kan kasashen biyu zuwa wani sabon mataki. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China