Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya jinjinawa shugaban jam'iyyar CPP ta kasar Cambodia
2020-07-03 20:54:07        cri
A yau Jumma'a ne babban sakataren jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kasar, mista Xi Jinping, ya aike da wani sako ga shugaban jam'iyyar CPP ta kasar Cambodia, kana firaministan kasar, mista Samdech Hun Sen.

A cikin sakon, shugaba Xi ya jinjinawa mista Hun Sen, bisa ziyarar da ya kawo kasar Sin a watan Fabrairun da ya gabata, yayin da kasar Sin ke cikin wani mawuyacin hali na fama da cutar COVID-19, lamarin da ya yi matukar burge jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da gwamnati da jama'ar kasar, da ma shi kansa shugaba Xi Jinping. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China