Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Matalauta Fiye Da 1500 Na Yankin Qianjiang Dake Birnin Chongqing Sun Koma Sabbin Gidaje
2020-07-03 21:08:05        cri

Wasu fama da kangin talauci fiye da 1500 wadanda suke rayuwa a cikin tsaunuka masu tsayi a yankin Qianjiang na birnin Chongqing, wato babban birnin dake karkashin jagorancin gwamnatin tsakiyar kasar Sin kai tsaye, sun samu tallafin gwamnati, inda a yanzu aka samar musu wasu sabbin gidaje dake garin Qianjiang, a wani mataki na fitar da su daga tsananin talauci.

Tun daga mazaunin su na tudu zuwa birni da suka koma, karamar gwamnatin Qianjiang ba ta dakatar da tallafin da take baiwa wadannan masu fama da talauci ba, inda take ci gaba da agaza musu, don kyautata yanayin zaman rayuwarsu.

A karshen shekarar bara, matalauta 1531 daga magidanta 413 na kauyuka ko gundumomi 29 a yankin Qianjiang, sun yi rajista bisa radin kansu, don komawa sabbin gidaje dake titin Chengnan na garin Qianjiang.

Darektan sashen jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a yankin Yu Changming, ya bayyana cewa, fitar da wadannan matalauta daga kangin talauci, aiki ne mai matukar wuya, saboda suna rayuwa cikin tsauni mai tsayi, kuma ta hanyar kwashe su zuwa sabbin gidaje, matakin zai taimaka musu, wajen fitowa daga kangin fatara kwata kwata.

An ce, akwai gonaki da suka kai fadin hekta 1.33 a kusa da sabbin gidaje nasu, an kuma rarraba su gida gida, an yi musu lamba.

Baya ga haka, an kafa cibiyar jiyya, da makarantar firamare, da gidan renon kananan yara, da dai sauran manyan ababen more rayuwa, an kuma kyautata yanayin su bisa bukata.

Lu Cuiju, wadda ta samu sauki daga cutar kansa mai tsanani, ta samu matukar kulawa, a lokuta da dama idan ba ta da lafiya, sai an tuntubi asibiti don kai mata dauki da wuri.

Wasu daga makaurata sun nuna cewa, lokacin da suke rayuwa a cikin tsaunuka, su kan kwashe sa'o'i 2 zuwa 3 a hanyar zuwa asibiti, amma yanzu za su iya isa gidan jinya cikin mintoci sha kawai. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China