Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'ar Johns Hopkins: adadin wadanda suka kamu da COVID-19 a duniya ya kai miliyan 11
2020-07-04 16:05:55        cri
Jami'ar Johns Hopkins ta Amurka, ta ce zuwa jiya Juma'a, adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a duniya ya zarce miliyan 11, inda ya kai miliyan 11,031,905.

Alkaluman cibiyar nazarin tsarukan kimiyya da injiniya ta jami'ar, sun nuna cewa, jimilar mutane 523,777 ne cutar ta yi ajalinsu a fadin duniya.

Kasar Amurka ce cutar ta fi yi wa illa, inda mutane 2,788,395 suka kamu, yayin da ta yi sanadin mutuwar 129,306. A kwanakin baya-bayan nan, ana ta samun karuwar mutanen da ke harbuwa da cutar a kasar a kullum, inda a ranar Alhamis, aka samu sama da mutum 52,000 da suka harbu.

Kasashen da adadin wadanda suka kamu da cutar ya zarce 250,000 sun hada da Brazil da Rasha da India da Peru da Chile da Birtaniya da kuma Spaniya. Cibiyar ta jami'ar Johns Hopkins ta kara da cewa, yawan wadanda suka kamu da cutar a wajen kasar Sin ya zarce miliyan 10.9. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China