Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kenya ta kaddamar da wani daftari mai kunshe da manufar shawo kan cutar sankara
2020-07-04 17:12:37        cri
Ma'aikatar lafiya ta kasar Kenya ta kaddamar da wata manufar yaki da cutar sankara ta 2019 zuwa 2030, domin taimakawa shawo kan cutar, wadda ke kara kamari a kasar.

Babban sakataren ma'aikatar lafiya ta kasar, Rashid Aman, ya ce ana sa ran manufar, ta taimaka wajen rage mace-mace, bisa la'akari da yadda ba a rasa mai cutar ko mai nasaba da mai ita a kowanne gida a kasar.

Rashid Aman ya kara da cewa, mutanen dake da cutar sankara, sun fi shiga hadarin kamuwa da cutar COVID-19. Inda ya ce daga cikin mutane 154 da suka mutu sanadiyyar COVID-19, 6 na jinyar cutar sankara a lokacin da suka mutu.

Ma'aikatar lafiya ta kasar, ta yi kiyasin cewa, al'ummar kasar 47,887 ne ke kamuwa da cutar a duk shekara, inda kuma take sanadin mutuwar 32,987 a kowacce shekarar.

Rashid Aman, wanda kuma ya kaddamar da rahoton binciken sankarar mama na farko, da aka yi wa lakabi da "gangamin wayar da kai game da sankarar mama", ya ce daftarin zai zama jagora wajen inganta ayyukan binciken sankarar mama a kasar.

Har ila yau, ya ce, sankarar mama ita ce ke kan gaba a kasar, inda a kowacce shekara ake samun sabbin mutane kimanin 6,000 dake kamuwa da ita. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China