Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An gano kwayar cutar Corona a cikin ruwan masai a watan Nuwamban bara a Brazil
2020-07-04 20:51:18        cri
Wata tawagar masu bincike daga jami'ar tarayya ta Santa Catarina ta Brazil, ta sanar da cewa, an samu wasu birbishin kwayoyin cutar Corona a ruwan masai, a watan Nuwamban bara a Florianopolis, babban birnin jihar Santa Catarina ta kasar.

Daga ranar 30 ga watan Oktoba, zuwa 4 ga watan Maris, tawagar masu binciken ta tattaro samfuran ruwan masai na wurare daban daban guda 6, a biranen Florianopolis da Santa Catalina.

Binciken nasu ya zo ne watanni 2 kafin a samu bullar na farko a hukumance a nahiyar Amurka a ranar 21 ga watan Junairu, haka kuma kafin samun bullar cutar a kasar, a karshen watan Fabreru.

Rahoto da tawagar masu binciken 14 ta fitar, ya ce sun gano kwayar cutar Corona a samfura 2 da suka samo a ranar 27 ga watan Nuwanban 2019, tun kafin a samu bullar cutar na farko a nahiyar Amurka.

Sun ce sakamakonsu ya nuna cewa, kwayar cutar ta yi ta bazuwa a Brazil tun cikin watan Nuwamban 2019, tun kafin samu bullarta a nahiya Amurka.

Baya ga Brazil, an gano kwayar cutar a ruwan masai a kasashen Spaniya da Italiya a bara tun kafin a samu bullar cutar na farko a Turai a farkon bana. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China