Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin Huawei a shirye yake ya tattauna da gwamnatin Birtaniya
2020-07-06 09:52:04        cri

Mahukuntan kamfanin Huawei mai hada hadar fasahar sadarwa dake kasar Sin, sun bayyana aniyar tattaunawa da tsagin kasar Birtaniya, tare da fatan ci gaba da musayar ra'ayi da abokan huldar su dake kasar, don magance tasirin takunkumin da Amurka ta ce za ta kakabawa kamfanin, ta yadda Birtaniya za ta kasance kan gaba, wajen cin gajiyar fasahar 5G mallakin kamfanin.

Tuni dai sashen cinikayya na gwamnatin Amurka, ya sanar da shirin kakabawa kamfanin na Huawei takunkumin sayen wasu kayan kirar hajojin da yake samarwa, wadanda wasu kamfanonin Amurka ke sarrafawa.

Wata sanarwa da kamfanin Huawei ya fitar a baya, ta ce sashen cinikayyar Amurka, ya ayyana shirin sanya takunkumin ne kawai domin lahanta moriyar Huawei.

Kaza lika tun a watan Janairun da ya shude, gwamnatin Birtaniya ta ayyana wani sabon shirin da ta kira da matakin tsaron sashen sadarwar ta, matakin da masharhanta ke kallo a matsayin kayyade rawar da kamfanin na Huawei ke takawa, wajen gina tsarin fasahar 5G a kasar.

To sai dai kuma, daga baya gwamnatin Birtaniyar ta ce tana sake nazari game da tasirin da takunkumin Amurka ka iya yi ga kamfanin, za kuma ta fitar da sanarwa kan hakan nan gaba cikin wannan wata na Yuli, kamar dai yadda wata kafar cikin gidan kasar ta bayyana. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China