Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Najeriya ya yi tir da harin Boko Haram kan jirgin MDD
2020-07-06 11:13:00        cri

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi tir da harin da mayakan Boko Haram suka kaddamar, kan wani jirgi mai saukar ungulu na jami'an MDD masu gudanar da ayyukan jin kai a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar.

Cikin wata sanarwa, shugaba Buhari ya yi Allah wadai da harin na ranar Asabar, wanda ya yi sanadiyyar hallaka fararen hula biyu, yana mai bayyana hakan a matsayin wani mummunan aiki na keta.

Ya ce wannan daya ne daga harin matsorata na baya bayan nan, kan jirgin kai agaji na MDD, kuma hakan na alamta irin yadda mayakan Boko Haram ke shan matsi daga dakarun sojin kasar, lamarin da ke tilasta musu aiwatar da irin wadannan hare hare na sari-ka-noke.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, jami'in tsare tsaren ayyukan MDD a Najeriya Edward Kallon, ya ce mayakan Boko Haram sun harbo jirgin kirar helikwafta ne a garin Damasak na jihar Borno, inda nan take ya fado, ya kuma hallaka mutane 2. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China