Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wata shaida mai kwari ta nuna cewa akwai kwayar cutar COVID-19 a Brazil tun Nuwamban bara
2020-07-06 13:26:12        cri

Wata tawagar masu bincike daga jami'ar tarayya ta Santa Catarina ta Brazil, ta sanar a ranar 2 ga wata cewa, daga watan Oktoban bara, zuwa Maris na bana, ta gudanar da bincike kan samfuran ruwan masai a Florianopolis, babban birnin jihar Santa Catarina ta kasar, inda a watan Nuwamban bara ta gano cewa, akwai kwayoyin cutar Corona a ruwan masan. Wannan ya zo ne watanni 2 kafin sanar da samun mutum na farko da aka tabbatar ya kamu da cutar a hukumance a nahiyar Amurka, haka kuma, watanni 3 kafin gwamnatin Brazil ta sanar da samun bullar cutar a kasar, a karshen watan Fabrerun bana.

Wannan bincike ya zama karin shaida mai karfi dake nuna cewa, an dade da samun cutar a kasashe da dama.

Da farko, jami'ar Barcelona ta Spaniya, ta fitar da wata sanarwa a ranar 26 ga watan Yuni, inda ta ce masu bincike a jami'ar sun gwada samfuran ruwan masai kuma sun gano cewa, akwai birbishin kwayar cutar COVID-19 a ruwan da suka tattara a ranar 12 ga watan Maris na shekarar 2019. Amma Spaniya ba ta ba da rahoton bullar cutar na farko ba sai a ranar 25 ga watan Fabrerun bana.

A baya, wata tawagar masu bincike daga jami'ar London da sauran kwalejoji, sun nazarci sinadaran kwayoyin cutar daga mutane sama da 7,500 da suka kamu da ita a fadin duniya, kuma sun yi ammana cewa, an samu sabbin kwayoyin cutar ne daga karshen shekarar 2019. Wannan ka iya zama lokacin da sabuwar kwayar cutar ta fara kama dan Adam daga sauran halittu, wato akwai yiwuwar kwayar cutar ta bazu a duniya ne a karshen shekarar 2019.

An samu barkewar sabuwar kwayar cutar a wurare da dama a fadin duniya, kuma bin diddigin cutar abu ne mai muhimmanci domin gano asalin yaduwarta, da yadda take rayuwa da bazaranar dake tattare da ita, da nufin daukar managartan matakan da suka dace na kandagarki da kuma dakile ta. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China