Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Kamaru ta musanta rahotanni dake cewa tana tattauna batun tsagaita bude wuta da shugabanni 'yan aware
2020-07-07 09:41:47        cri

Gwamnatin Kamaru ta musanta rahotanni game da tattaunawar tsagaita bude wuta tsakaninta da shugabannin 'yan aware dake tsare.

Wannan na zuwa ne bayan shugabannin 'yan aware dake zaman daurin rai da rai, sun bayyana a ranar Juma'a cewa, sun fara tattaunawar tsagaita bude wuta da gwamnatin kasar, sai dai ba su yi karin haske game da tattaunawar ba.

Ministan sadarwa kuma kakakin gwamnatin kasar, Emmanuel Rene Sadi, ya ce har yanzu gwamnati na maraba da hawa teburin sulhu da nufin kawo karshen rikicin 'yan aware da ya shafe sama da shekaru 3 a yankunan kasar biyu na arewa maso yamma da kudu maso yamma, wadanda ke da rinjayen masu amfani da harshen Ingilishi.

Ya kara da cewa, sojoji za su ci gaba da tsaron al'umma da dukiyoyinsu a yankunan, bisa kwarewa.

Tun cikin shekarar 2017, dakarun gwamnati da 'yan aware masu dauke da makamai ke fafatawa, bayan 'yan awaren sun ayyana 'yancin kan yankunan biyu masu amfani da Turanci. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China