Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta ce mutane miliyan 3.5 za su fuskanci karancin abinci a Somaliya
2020-07-07 09:56:46        cri
Hukumar kula da ayyukan jinkan bil Adama ta MDD ta bayyana cewa, akwai yiwuwar mutane miliyan 3 da rabi za su iya tsunduma cikin matsalar karancin abinci a kasar Somaliya tsakanin watan Yuni zuwa Satumbar wannan shekarar.

Ofishin ayyukan jin kai na MDD, OCHA, ya ce akwai kuma yara sama da miliyan guda da aka yi hasashen za su iya fuskantar matsalar karancin abinci mai gina jiki.

Rahoton OCHA na baya bayan nan ya nuna cewa, mai yiwuwa ne wasu mutanen kimanin miliyan 2.6 za su ci gaba da zama a cikin yanayin kauracewa muhallansu, sannan wasu yara 'yan makaranta kusan miliyan daya za su ci gaba da zaman dirshan sakamakon matsalolin rufe makarantu wanda annobar COVID-19 ta haddasa.

MDD ta ce tun a ranar 16 ga watan Maris bayan samun rahoton farko na bullar cutar COVID-19 a Mogadishu, matsaloli ninki uku da suka hada da barazanar barkewar annobar, da ambaliyar ruwa, da kuma bayyanar farin dango, sun jefa kasar Somaliya cikin halin rashin tabbas, lamarin da ya haifar da matsaloli ga shirin ayyukan jinkan bil adama a kasar.

Matsalolin sauyin yanayi, hare-haren 'yan bindiga a shekaru da dama, gami da karuwar talauci, sun jefa rayuwar mutanen kasar Somaliya miliyan 5.2 cikin yanayin neman agaji a shekarar 2020. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China