Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya za ta ci gaba da karfafa kyakkyawar dangantaka da kasar Sin
2020-07-07 10:04:13        cri
Gwamnatin Najeriya ta yi alkawarin ci gaba da tabbatar da dorewa kyakkyawar dangantakar da aka jima da gina ta a tsakaninta da kasar Sin.

Zubairu Dada, karamin ministan harkokin kasashen wajen Najeriyar, shi ne ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakuncin jakadan kasar Sin dake Najeriya mai barin gado, Zhou Pingjian a ofishinsa dake Abuja, babban birnin kasar.

Ministan ya taya jakadan mai barin gado murnar samun nasarar kammala aikinsa a Najeriya, inda ya bayyana shekaru ukun da jakadan ya shafe a kasar a matsayin muhimmiyar nasara mai cike da kyawawan sakamako.

Ya ce sadaukar da kai da kuma jajurcewar da mista Zhou ya nuna a tsawon wa'adin zamansa a Najeriya, ya taimaka matuka wajen inganta kyakkyawar alakar dake tsakanin Najeriya da Sin.

Minisatan ya yi alkawarin ci gaba da daukar matakan da za su tabbatar da karfafa kyakkyawar dangantaka a tsakanin kasashen biyu. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China