Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin ya gabatar da bukatar shiga yarjejeniyar cinikin makamai ga babban sakataren MDD
2020-07-07 10:18:13        cri

Zhang Jun, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, ya gabatar da bukatar shiga yarjejeniyar cinikin makamai ta ATT ta kasar Sin ga babban sakataren MDD Antonio Guterres a ranar Litinin.

Da yake gabatar da bukatar, Zhang ya ce, gwamnatin kasar Sin tana dora muhimmanci game da matsalolin da fasa kaurin makamai da kuma saba yarjejeniyar cinikin makamai ke haifarwa. Kasar Sin tana goyon bayan manufofin yarjejeniyar kuma ta amince da daukar dukkan matakan da suka dace wajen kiyaye dokokin kasa da kasa dake shafar cinikin makamai da batun kawar da fasa kaurin makamai.

Bugu da kari, kasar Sin a ko da yaushe tana daukar tsauraran dokoki yayin fitar da kayayyakin aikin soji zuwa ketare, bisa ma'aunin yarjejeniyar cinikin makamai ta ATT.

Jakadan na Sin ya ce, shiga yarjejeniyar ATT wani muhimmin mataki ne da kasar Sin ta dauka domin daidaita batutuwan dake shafar cinikin makamai na kasa da kasa, da kuma kiyaye tsaro da zaman lafiyar kasa da kasa da shiyyoyin duniya.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China