Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanan kasa da kasa: dokar kiyaye tsaron yankin Hongkong ta kyautata dokar kiyaye tsaron kasar Sin
2020-07-07 11:29:20        cri
Masanan kasa da kasa sun bayyana a kwanakin baya cewa, dokar kiyaye tsaron yankin Hongkong ta kyautata dokar kiyaye tsaron kasar Sin da ake aiwatar da ita a yankin, wanda hakan zai tabbatar da zaman lafiya da wadata mai dorewa a yankin.

Masanin kasar Faransa mai kula da batutuwan Sin Pierre Picquart ya bayyana cewa, ya kamata a dakatar da nuna ra'ayi mai cike da kuskure ga kasar Sin, tare da lura da hakikanin batun dake faruwa a kasar. Pierre Picquart ya ce kasar Sin ta yanke hukunci kan ayyukan tada rikice-rikice da karfin tuwo ta hanyar kafa doka.

Masanin ya kara da cewa, duk wani mataki na ayyukan lalata odar zamantakewar al'umma dake faruwa a yankin Hongkong, daidai yake da nuna goyon bayan tsattsauran ra'ayi, kuma hakan ba shi da bambanci da abun dake faruwa a kasashen Turai, ko sauran wasu sassan duniya.

A nasa bangare kuwa, Forfesa Garth le Paire na jami'ar Pretoria ta kasar Afirka ta Kudu ya bayyana cewa, "manufar kasa daya mai bin tsarin mulki biyu", ta tabbatar da yankin Hongkong, a matsayin yanki na musamman na kasar Sin. Kuma Sin tana da ikon tsara dokar kiyaye tsaron yankin Hongkong daga fannonin dokoki, ko yanayin da ake ciki. Ya ce gwamnatin kasar Sin ta dauki alhakin taimakawa yankin Hongkong wajen mayar da zaman lafiya da na karko, da kuma magance tsanantar yanayin yankin. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China