Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kawar da talauci ta hanyar shuka fure
2020-07-07 14:18:46        cri

Jami'in kula da yaki da talauci mai suna Chen Hua mai shekaru 61 da haihuwa, ya fara aikin yaki da talauci a shekarar 2006, kuma ya gudanar da ayyukan yaki da talauci a kauyuka 8 dake garuruwa 7, a lardin Heilongjiang na kasar Sin, inda mazauna kauyukan ke kiran sa da sunan Malam Chen.

A sakamakon samun fasahohin yaki da talauci, malam Chen ya taimakawa mazauna kauyukan dabarun kyautata tsarin shuke-shuke, da fara raya sha'anin yaki da talauci ta hanyar shuka fure. Kana ya kafa rukunin injuna don yin shuke-shuke ta amfani da injunan a kan kasa mai fadin kimanin hektoci 700 a kauyen. Haka zalika kuma, ya kafa sabuwar tashar samar da wutar lantarki mai aikin hasken rana, don tabbatar da zaman yau da kullum na mutane mafiya fama da talauci.

Malam Chen ya bayyana cewa, ba ya son ganin mutane sun shiga cikin halin fama da talauci, maimakon haka yana son taimaka musu wajen kawar da talauci. A duk lokacin da ya tashi daga wani kauye wanda ya samu babban canji, yana jin matukar farin ciki sosai, don haka aka ci gaba da dora masa nauyin ci gaba da yin wannan aiki. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China