Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin a Birtaniya: Dokar tsaron kasa a yankin Hong Kong na kasar Sin ta dace da manufar "kasa daya da tsarin mulki biyu"
2020-07-07 14:51:25        cri

A ranar 6 ga wata bisa agogon wurin, jakadan kasar Sin da ke Birtaniya Liu Xiaoming, ya kira taron manema labarai na gida da na waje ta kafar bidiyo a ofishinsa, inda ya bayyana matsayin gwamnatin kasar Sin kan dokar tsaron kasa a yankin Hong Kong. Jakada Liu ya nuna cewa, yadda aka kafa dokar tsaron kasa a yankin Hong Kong don kyautata tsarin dokokin yankin, na tabbatar da tsaron kasa, da ma tsarin aiwatar da dokokin na iya biyan bukatun jama'a, don haka ya zama dole a kafa ta cikin gagawa. Liu ya kara da cewa,

"Wannan doka ta dace da manufar 'kasa daya da tsarin mulki biyu', wadda kuma za ta taimaka wajen tabbatar da aiwatar da manufar yadda ya kamata cikin dogon lokaci. A cikin dokar tsaron kasa a yankin Hong Kong, an tanadi cewa, za a tsaya tsayin daka wajen bin manufofin 'kasa daya da tsarin mulki biyu' da 'mazauna yankin Hong Kong, na da 'yancin gudanar da harkokin kansu'. 'Kasa daya' tushe ne na bin 'tsarin mulki biyu', kuma idan ba a amince da manufar 'kasa daya' ba, to babu bukatar a ambaci bin 'tsarin mulki biyu'. Muddin aka tabbatar da tsaron kasar, hakan zai iya ba da tabbaci ga aiwatar da manufar 'tsarin mulki biyu'."

Ban da wannan kuma, Jakada Liu ya nuna cewa, ana ta da tarzoma a yankin Hong Kong, bisa nufin kawo cikas ga aikin aiwatar da manufar "kasa daya da tsarin mulki biyu", lamarin da ya sa aka fitar da dokar tsaron kasa a yankin Hong Kong, bisa aniyar kiyaye manufar "kasa daya da tsarin mulki biyu", da ma kyautata manufar, a maimakon canja manufar. Liu yana mai cewa,

"Yadda aka kafa dokar ya shaida daidaituwar ikon gudanarwa daga dukkan fannoni da gwamnatin tsakiya ke da shi, da ikon cin gashin kai da Hong Kong ke da shi, wanda ba zai canja tsarin jari hujja da Hong Kong ke bi a yanzu ba, ba zai kuma canja manufar cin gashin kai da dokokin yankin da Hong Kong ke aiwatarwa ba. Haka kuma, ba zai ba da tasiri ga ikon gudanar da harkokin gwamnatin yankin, da ikon kafa doka, da ikon shari'a, da ma ikon karshe na yanke hukunci da Hong Kong ke da su ba."

Haka zakila ma dai, Jakada Liu Xiaoming ya furta cewa, kasar Birtaniya ta sa "Sanarwar hadin kan Sin da Birtaniya" da manufar "kasa daya da tsarin mulki biyu" a rude suke, har ma ta zargi kasar Sin da gaza sauke nauyin da ke wuyanta, lallai wannan kurkure ne. Liu ya ce,

"Game da manufar 'kasa daya da tsarin mulki biyu' ta gwamnatin kasar Sin, ana iya gano su sosai a cikin babbar dokar yankin musamman na Hong Kong, haka kuma, ana aiwatar da ita yadda ya kamata. Don haka, babu batun cewa wai kasar Sin ba ta sauke nauyin da ke wuyanta ba."

A karshe dai, Jakada Liu ya jaddada cewa, bayan komawar Hong Kong kasar Sin, Birtaniya ba ta da ikon mulki, da ikon gudanarwa, da ma ikon sanya ido a yankin. Amma ba sau daya ba sau biyu ba, gwamnatin Birtaniya ta sha bayar da rahotanni kan batun Hong Kong a duk rabin shakara, domin yin tsegumi kan harkokin yankin. Yanzu kuma ta fara tsoma baki kan dokar tsaron kasa a yankin, har ma ta ce wai za ta bai wa 'yan yankin HK masu mallakar Fasfon Birtaniya na 'yan kasashen waje, damar zama a Birtaniya. Lallai abin da Birtaniya ta yi ta tsoma baki cikin harkokin gidan Sin, da ma karya ka'idojin kasa da kasa, don haka Sin ta nuna rashin jin dadinta, da ma rashin yardarta kan wannan batu. Liu ya ce,

"Abin da nake so na jaddada a nan shi ne, Hong Kong wani yanki ne na kasar Sin, kuma harkokin Hong Kong harkokin cikin gida ne na Sin, kuma babu wata kasa da take da ikon tsoma baki a ciki. Wani muhimmin aiki na dokar tsaron kasa a yankin Hong Kong shi ne, kandagarki da shawo kai, da ma hukunta wadanda ke hada baki da ketare, wajen illata tsaron yankin. Bai dace a raina aniyar Sin ta kiyaye ikon mulkinta, da tsaronta, da ma ci gabanta ba. Kaza lika duk wani yunkuri na neman kawo cikas ga aiwatar da dokar tsaron kasa a yankin Hong Kong, zai gamu da kiyayya daga al'ummar Sin bililyan 1.4, wanda kuma tabbas zai bi ruwa." (Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China