Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi taron ministocin dandalin hadin-gwiwar kasar Sin da kasashen Larabawa karo na 9
2020-07-07 19:19:14        cri
Jiya Litinin, an yi taron ministocin dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar kasar Sin da kasashen Larabawa karo na 9 ta kafar bidiyo, inda aka fitar da wasu sanarwa, ciki har da "Hadaddiyar Sanarwa" kan dakile annobar COVID-19 cikin hadin-gwiwa, da "Sanarwar Amman", da takardar nasarori na shirye-shiryen ayyuka da ake fatan gudanarwa nan da shekaru biyu masu zuwa. A yau talata, ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta kira taron manema labarai dangane da wannan taron.

A nasa bangaren, shugaban sashin harkokin yammacin Asiya da arewacin Afirka na ma'aikatar, Wang Di ya bayyana cewa, a yayin taron, Sin da kasashen Larabawa sun yi musanyar ra'ayoyi kan yadda za su yi kokarin yaukaka dangantakar abokantakarsu bisa manyan tsare-tsare, da raya al'ummarsu mai kyakkyawar makoma ta bai daya .

Wang Di ya kara da cewa, a sanarwar da aka fitar, kasashen Larabawa sun nuna tsayayyen goyon-bayansu ga matsayin gwamnatin kasar Sin kan batun yankin Hong Kong, da kokarin da kasar take wajen kare tsaronta karkashin manufar "kasa daya amma tsarin mulki biyu". Kasashen Larabawan suna kuma adawa da yin shisshigi a harkokin cikin gidan kasar Sin, da tsayawa kan manufar kasar Sin daya tak a duniya, da kin yarda da balle yankin Taiwan daga kasar, tare kuma da marawa kasar baya wajen daukar matakan yakar ayyukan ta'addanci da kawar da masu tsattsauran ra'ayi, da kin yarda da duk wani yunkurin da ake na kawowa kasar Sin baraka.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China