2020-07-07 20:11:11 cri |
Rikicin da ya barke a kan iyakokin Sin da Indiya a watan Afrilu, ya jawo hankalin kasa da kasa. A matsayinsu na makwabtan juna, tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kan iyakokin kasashen biyu, ya dace da muradunsu dukka, kuma samun ci gaban kasa shi ne babban aiki mafi muhimmanci ga kasashen biyu. Alal misali, kasar Sin tana shirin kawar da kangin talauci baki daya a karshen shekarar da muke ciki, da cimma burin raya al'ummar kasar mai matsakaicin wadata, tare kuma da habaka bude kofarta ga kasashen waje daga dukkan fannoni. Ita ma kasar Indiya, tana shirin raya tattalin arzikinta da darajarsa zata kai dala triliyan 5 zuwa nan da shekarar 2025, abun da ya sa kasar zama daya daga cikin kasashe mafi karfin tattalin arziki a duniya. Ganin yadda kasashen biyu ke da kamanceceniya da dama a fannin neman bunkasuwa, ya zama dole su dakatar da yiwa juna barazana, a maimakon haka, su karfafa hadin-gwiwa.
Musamman a daidai wannan lokaci da cutar COVID-19 ke dada bazuwa a fadin duniya, akwai kasashe da dama ciki har da Indiya, wadanda suke fuskantar babban matsin lamba a fannonin da suka jibanci dakile yaduwar cutar da farfado da tattalin arziki, don haka, duk wani yunkuri na lalata dangantakar Sin da Indiya zai iya tsananta halin da ake ciki.
A dayan bangaren kuma, Sin da Indiya muhimman kasashe ne wadanda suka taimaka sosai ga habakar tattalin arzikin duniya, wato idan sun iya daidaita sabanin dake tsakaninsu da kara gudanar da shawarwari, hakan zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya baki daya. (Murtala Zhang)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China