Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Uwargidan shugaban kasar Sin ta mika sako ga kungiyar OAFLAD domin goyon-bayan Afirka na yakar COVID-19
2020-07-07 20:35:16        cri

Uwargidan shugaban kasar Sin Madam Peng Liyuan ta aikawa shugabar kungiyar neman ci gaba ta matan shugabannin kasashen Afirka ko kuma OAFLAD a takaice ta wannan zagaye, kana uwargidan shugaban Kongo(Brazzaville) madam Antoinette Sassou Nguesso, gami da sauran matan shugabannin kasashen Afirka wasika, inda ta godewa kasashen Afirka saboda babban goyon-bayan da suka nuna wa jama'ar kasar Sin a lokacin da take cikin mawuyacin hali na yaki da annobar COVID-19, tare da mika gaisuwa da fatan alheri ga al'ummar nahiyar Afirka baki daya.

Madam Peng Liyuan ta bayyana cewa, bayan barkewar annobar COVID-19 ba zato ba tsammani, ya zama dole kasa da kasa su taimaki juna da fadada hadin-gwiwa domin ganin bayan annobar. Gwamnatin kasar Sin za ta samarwa kasashe 53 dake nahiyar Afirka wasu kayan agaji ta hannun kungiyar OAFLAD, a wani kokari na tallafawa mata da yara da kuma matasa, domin shaida zumuncin dake tsakanin al'ummomin Sin da Afirka.

A kwanan nan ne, madam Antoinette Sassou Nguesso ta aiko da sako ga madam Peng Liyuan, inda ta jinjinawa kasar Sin saboda muhimmiyar rawar da ta taka wajen dakile cutar COVID-19, kana, a madadin matan shugabannin kasashe membobin kungiyar OAFLAD, madam Antoinette ta bukaci kasar Sin da ta maida hankali kan mata da yara da matasan Afirka, tare kuma da ba su kayan aikin jinya.

An tura kayan tallafin da kasar Sin ta samar zuwa kasashen Afirka daban-daban, inda madam Antoinette Sassou Nguesso da wasu manyan jami'an gwamnatin kasashen Afirka suka halarci bikin, suka bayyana cewa, irin wannan abun da kasar Sin ta yi ya shaida dadadden zumunci dake tsakanin Afirka da kasar Sin.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China