Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta kammala dukkan ka'idojin shiga yarjejeniyar cinikayyar makamai ta kasa da kasa
2020-07-07 20:41:13        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya shaidawa taron manema labarai Talatar nan cewa, kudirin kasar Sin na shiga yarjejeniyar cinikayyar makamai, wani muhimmin mataki ga kasar na ganin ana damawa da ita kan yadda ake cinikayyar makamai a duniya da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya da shiyya-shiyya.

Bugu da kari, matakin ya alamta kudirin kasar na goyon bayan tsarin kasancewar bangarori daban-daban, da kiyaye tsarin makamai na kasa da kasa, da gudanar da tsarin gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adam.

A jiya ne zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya gabatar da bukatar kasarsa na shiga yarjejeniyar cinikayyar makamai ga babban sakataren MDD a hedkwatar majalisar. Zhang Jun ya ce, matakin na kasar Sin, shi ne cikamakin dukkan ka'idojoji na doka dake baiwa kasar damar shiga wannan yarjejeniya, wadda za ta fara aiki cikin kwanaki 90 daga jiyan.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China