2020-07-07 21:00:35 cri |
Ana dai daukar abin da ya faru a ranar 7 ga watan Yulin shekarar 1937 a gadar Logou, a matsayin mafarin hare-haren da Japan ta yiwa kasar Sin, kuma baki dayan al'ummar kasar suka nuna turjiya.
Lamarin na ranar Talata ya faru a kusa da gadar, a dakin ajiye kayan tarihi na yakin al'ummar Sinawa kan maharan Japanawa.
Sama da mutane 200, ciki har da mambobin iyalan shugabannin sojoji da wadanda suka yi shahada a yaki ne, suka halarci bikin.
Mutane sun ajiye furanni tare da sunkuyawa don nuna gimamawa ga wadanda suka mutu a yakin kin kutsen Japanawa da ya faru sama da shekaru 80 da suka gabata.
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China