Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Isra'ila: Janye jiki daga WHO da Amurka ta yi zai lahanta kokarin da duniya ke yi na yakar COVID-19
2020-07-10 14:49:29        cri

Kwanan baya, Amurka ta sanar da MDD cewa, tana aiwatar da shirin janye jiki daga hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO.

Game da hakan, wani masani na kasar Isra'ila mai suna Alexander B Pevzner ya nuna cewa, janye jiki daga WHO da Amurka ta yi, mataki ne na gaza sauke nauyin dake wuyanta, kuma babu basira a ciki, kana zai lahanta kokarin da duniya ke yi wajen yakar COVID-19.

A kwanan nan, masanin kasar Isra'ila Alexander B Pevzner ya zanta da manema labarai na babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG da harshen Sinanci, inda ya nuna cewa, ya zuwa yauzu, cutar COVID-19 na yaduwa a duk fadin duniya, karin mutanen da suka kamu da wannan cutar a Isra'ila a ko wace rana ya kai fiye da 1000, kuma halin da Amurka, da nahiyar Turai, da kuma Latin Amurka na kara tsananta, ana cikin wani muhimmin lokaci na yakar COVID-19, amma Amurka ta sanar da janye jikinta daga hukumar kiwon lafiya ta duniya ta WHO a wannan lokaci, mataki ne na maras kyau. Ya ce:

"Ba mu samu nasara a kan wannan cutar ba tukuna, ana kokarin magance wannan matsala amma Amurka ta sanar da janye jiki daga WHO, a gani na, matakin da Amurka ke dauka maras kyau ne, kuma gudun sauke nauyin dake wuyanta ne, saboda ana bukatar hadin kan kasa da kasa don yakar wannan cutar. A wani bangare na daban kuwa, ana kokarin fitar da allurar rigakafin cutar. Kasancewar wannan kwayar cuta sabuwa ce, hakan ya sa ake bukatar sabuwar allura. A gani na, Amurka ta gaza ba da gudunmawarta a wannan fanni, wanda hakan ke da ban mamaki. Kamar dai wani abun da babu ruwan Amurkar a ciki, tana gujewa sauke nauyin dake wuyanta."

Ban da wannan kuma, Alexander B Pevzner ya ce, ko da yake, Amurka tana sahon gaba a duniya a fannin tsarin ba da jiyya, amma ba ta iya ware kanta daga duniya. A hakika dai, cutar ta yi kamari a Amurka, mutane da dama sun rasa rayukansu a kasar. Ya ce:

"Watakila Amurka tana ganin cewa, tsarin kiwon lafiyar ta na da inganci sosai, saboda tana da nagartattun likitoci da asibitoci, tana da kudade masu dimbin yawa, kasa ce mai wadata sosai. Amma, kowa ya sani, ba dukkanin Amurkawa ne ke da damar samun jiyya mai kyau. A wani bangare kuma, akwai matsalar kudade, wato batun ko za a iya samun jiyya ko a'a, ya danganta da ko ana da inshorar jiyya ko a'a. Kana a wani bangare na daban kuwa, yana danganta da ina ake zaune. Idan kana zaune a birnin New York, to, za ka iya samun jiyya, ganin kasancewar nagartattun asibitoci da dama a wurin, amma a wasu kananan garuruwa, ta yaya Amurkawa dake wuraren za su samu jiyya?"

A ganin Alexander B Pevzner, matakin da Amurka ta dauka na janye jikinta daga WHO, mataki ne na gudun saukar nauyin dake wuyanta, kuma zai lahanta moriyar Amurka ita kanta. Ya ce:

"Amurka ba ta shawo kan matsalarta ba a fannin yakar cutar, amma tana son janye jikinta daga WHO. Lallai ban san dalilin daukar wannan mataki ba. Watalika irin wannan wasa ne take yi a siyasance, domin ta bayyanawa magoyanta cewa, ba za ta mika kai ga ko wace kungiya ba ciki hadda WHO, mataki ne rashin wayewar kai. Amurka ta sanar da janye jikinta daga ayyukan WHO, da zummar kin yarda da biyan kudi ga WHO, mataki ne na yin tsimin kudi. Amma, kamar yadda a kan ce, a toya mai a mance da albasa. Duk da cewa ta yi tsimin wasu kudi, amma za ta kara samun asarar kudade saboda saurin yaduwar cutar a cikin kasar, inda yawan kudin da za ta yi asara zai fi na kudin da za ta baiwa WHO. A ganina, wannan mataki babu kyau kuma babu imani."

Ban da wannan kuma, Alexander B Pevzner ya nuna cewa, Babu bambancin kasa da kasa a gaban cutar COVID-19, ya kamata kasashen duniya sun hada kansu don yakar cutar tare. Idan a dauki mataki bisa kashin kansa, to, za a lahanta muradun duk fadin duniya ciki har da na Amurka. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China