Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan Mali ya sanar da aniyar kafa gwamnati hadaka a nan gaba kadan
2020-07-13 13:48:55        cri
Firaministan kasar Mali Boubou Cisse, ya sanar a ranar 11 ga wata cewa zai kafa gwamnatin hadin gwiwa nan ba da jimawa ba domin warware dambarwar siyasa da rikice-rikicen dake fuskantar kasar Mali.

Boubou Cisse ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci mutanen da suka ji raunuka a lokacin zanga-zangar da ta barke a ranar 10 ga wata a Bamako, babban birnin kasar ta Mali. A ranar 10 ga wata ne gamayyar kungiyoyin 'yan adawa na June 5 Movement-Patriotic Force Union, suka gudanar da zanga-zanga a birnin Bamako, inda suka bukaci shugaban kasar Mali Ibrahim Boubakar Keita ya yi murabus. Daga bisani zanga zangar ta rike ta koma tashin hankali. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China