Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: Ya kamata a kara kaimin yaki da COVID-19 a yankuna marasa galihu na Afrika
2020-07-17 10:14:25        cri
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta bukaci a kara azama game da daukar matakan rage tasirin annobar COVID-19 a yankunan da suka fi tsananin bukatar tallafin jin kan bil adama a dukkan yankunan kudu da hamadar Sahara dake Afrika domin rage munanan illolin da matsalar ka iya haifarwa.

Matshidiso Moeti, daraktar hukumar WHO ta shiyyar Afrika, ta ce al'ummomin dake fama da matsalolin tashe tashen hankula da bala'u daga indallahi a nahiyar suna bukatar kulawa ta musamman wanda ya dace a baiwa mutanen marasa galihu a yayin da ake yaki da annobar COVID-19.

Yankin kudu da hamadar Sahara dake Afrika yana da sama da kashi 26 bisa 100 na yawan 'yan gudun hijira na duniya baki daya, kuma akwai kimanin mutane miliyan 19 wadanda rikice rikice ya tilastawa ficewa daga matsugunansu.

Ta bukaci a kara zuba kudade masu yawa a fannin gwaje gwajen cutar COVID-19, da warware matsalolin mutanen da tashe tashen hankula ya shafa a Afrika.

Moeti ta ce, a wannan mako an sabunta shirin samar da agajin MDD da nufin bunkasa shirin yaki da annobar COVID-19 a sansanonin 'yan gudun hijira dake fadin Afrika ta hanyar samar da tsabtaccen ruwan sha, da abinci, da kuma tallafin kayayyakin hada abinci masu gina jiki.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China