Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An Yiwa Gine-Ginen Gargajiya Gyaran Fuska Ba Tare Da Lalata Al'Adu Ba Don Kara Ingancin Zaman Rayuwar Jama'A
2020-07-20 14:55:34        cri

 

Shekarar nan ta 2020, shekara ce mai muhimmanci game da kawar da talauci a duk fadin kasar Sin. Yankunan dake fama da talauci a nan kasar Sin na canjawa matuka karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, matakin da ya sa al'ummar Sinawa ke hada kansu, don tabbatar da zaman al'umma mai matsakaicin karfi.

Shugaba Xi Jinping ya taba bayyana cewa, lokacin da ake kokarin kyautata zaman rayuwar jama'a, bai kamata an yi asarar al'adun gargajiya ba, wato ya dace a yiwa wasu gine-ginen gargajiya gyaran fuska ba tare da lalata al'adu ba. Yauzu haka, ana kokarin kyautata wasu titunan gargajiya dake birnin Guangzhou yadda ya kamata.

Kwanakin baya-bayan nan, an yiwa titin gargajiya da aka gada daga kaka kakkani na farko na birnin Guangzhou kwaskwarima, wanda shi ne muhimmin mataki daga cikin titunan Yongqingfang ta yankin Xiguan da ake yiwa gyara fuska a mataki na biyu, za kuma a kammala wannan aiki cikin gajeren lokaci. Wani mazaunin wuri ta ce:

"Muna zaune a wannan wuri tun lokacin da muke kanana, har zuwa yanzu shekaru 60 ke nan da suka gabata, muna farin ciki matuka domin ganin irin wadannan sauye- sauye."

Tituan Yongqingfang tana kudu maso yammacin birnin Guangzhou, yanki ne mafi wadata a lokacin da. Amma sun kasa samun gyara saboda tsakiyar birni ya sauya zuwa gabas. Yiwa wannan wuri gyaran fuska ba ma kawai aikin zamanitar da birni ba ne, har ma mataki ne dake kyautata zaman rayuwar wurin. A shekarar 2016, an yanke shawarar yiwa wadannan titunan gyaran fuska a mataki na farko ba tare da lalata wasu gine-gine na gargajiya ba. Mai nazari Jiang Wanghui ya ce:

"Ka duba, ba a cire wadannan tubali na gargajiya ba, mun yi musu jiki na karfe don su kara inganci. Ta wannan hanya mun kiyaye halayen gine-gine na gargajiya."

Ran 24 ga watan Oktomba na shekarar 2018, shugaba Xi Jinping ya taba ziyartar wannan wuri, inda ya nanata cewa, ya kamata a mai da hankali matuka ga kiyaye al'adu yayin da ake kokarin kyautata birane, kada a gudanar da wannan aiki cikin sauri. Dole ne a mai da hankali kan kyautata halin zaman rayuwar jama'a, da yiwa wadannan wurare gyaren fuska ba tare da lalata gine-ginen gargajiya ba.
Bisa bukatun shugaba Xi, an yiwa wadannan wurare gyaran fuska, an kawar da koma baya, kuma an kiyaye al'adu. Lokacin da ake yiwa wani gini gyaran fuska, ana kiyaye halayen tagogi na ice da gilashi, ta hanyar shafa musu fenti kawai, da kuma kiyaye kayayyakin sassaka masu launuka ta hanyar sake yi musu launuka sannu a hankali. Jiang Wanghui ya ce:

"Muna gyara wadannan gine-gine na gargajiya sannu a hankali, kamar aikin surfani, da zummar kyautata zaman rayuwar jama'a a wurin, matakin da zai taimaka wajen dakatar da koma bayan tituna na gargajiya, da samar musu kuzari bisa zamani."
An ce, titunan Yongqingfang, wuri ne da masu fasahar wasan kwaikwayo iri na lardin Guangdong wato Yueju suka taru a lokacin da, saboda haka akwai al'adun Yueju matuka a wurin. An gina wani dakin adana kayayyakin gargajiya na Yueju bisa salon gargajiya, don biyan bukatun mazaunan wuri. Mutane da dama suna zuwa wannan wuri don shakatawa, da kallo wasan kwaikwayo na Yueju a ko wace rana.

Dadin dadawa, titunan da aka yiwa gyaran fuska a mataki na farko, sun jawo hankalin 'yan kasuwa har 60 a fannonin aikin kirkire-kirkire ta fuskar al'adu, da gidajen kwana, da dakunan cin abinci, da kamfanonin raya al'adu da dai sauransu, hakan ya sa titunan sun zama mahadar al'adu a bangarori daban-daban. Mai fasahar samar da kayayyakin tagula a yankin Xiguan Wu Daming ya ce:

"Gwamnatin ta kyautata muhalli da kuma wurare, abin da ya ba mu kwarin gwiwa matuka, abin dake gabanmu, shi ne gudanar da ayyukanmu yadda ya kamata."
An ce, wannan aiki a mataki na farko ya kyautata tsoffin unguwanni har 380, inda a cikin mataki na biyu da ake aiwatarwa, iyalai dubu 490 masu kunshe da mutane miliyan 1.57 za su ci gajiyar aikin. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China