Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta nemi a kawo karshen girke sojoji a Sirte na Libya tare da tsagaita bude wuta
2020-07-21 13:10:38        cri
Biyo bayan karuwar dakarun da suka kewaye birnin Sirte, MDD na bukatar dukkan masu ruwa da tsaki su tsagaita bude wuta a Libya, maimakon kara rura wutar rikici.

Sakatare janar na majalisar Antonio Guterres, ya bayyana ta bakin kakakinsa Stephane Dujarric cewa, babu wani matakin soji da zai shawo kan rikicin da ake fuskanta a Libya, yana mai cewa dole ne a tsagaita bude wuta nan take. Ya kara da cewa, suna ci gaba da kira ga kasashen duniya, da su taimakawa al'ummar Libya cimma matsayar da zata kai ga tsagaita bude wuta mai dorewa.

Stephane Dujarric ya ce kamata ya yi cimma wannan matsaya ta kasance karkashin jagorancin shirin MDD.

Kiran na MDD na zuwa ne bayan majalisar dokokin Masar, ta fara duba yuwuwar tura dakaru yankin yammacin kasar dake iyaka da Libya. A lokaci guda kuma, ana samun karuwar sojoji a kewayen birnin Sirte, wanda tun watan Janairun bana ke karkashin ikon rundunar sojin dake adawa da gwamnatin kasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China