Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabannin jamiyyun siyasar kasashen duniya na goyon bayan kokarin Sin na kare zaman lafiya da ci gaban Hong Kong
2020-07-22 10:36:24        cri

Shugabannin jam'iyyun kasashen duniya sun bayyana adawarsu da matakin Amurka na zartar da dokar da take ikirarin na 'yancin cin gashin kai ne ga yankin Hong Kong, inda kuma suka bayyana goyon bayansu ga dokar tsaron kasar Sin kan yankinta na HK, dake da nufin kare cikakken ikonta da muradunta na tsaro da ci gaba.

Mohamed Bazoum, shugaban jam'iyyar NPDS ta Niger, ya ce zartar da dokar, batu ne na cikin gidan kasar Sin, kuma babu wata kasa dake da 'yancin tsoma baki ciki.

Ya ce an dade wasu kasashe suna fakewa da batun hakkin bil adama, suna tsoma baki cikin harkokin gidan wasu kasashe, amma kuma suke watsi da na su matsaloli. Ya kara da cewa, Niger na goyon bayan kasar Sin wajen aiwatar da dokar tsaro a HK, bisa tanadin kundin tsarin kasar da dokokin HK.

Shi ma Moussa Timbine, shugaban majalisar dokokin kasar Mali cewa ya yi, harkokin HK, harkoki ne na cikin gidan kasar Sin, yana mai cewa, kare tsaro da kwanciyar hankali a yankin, hakki ne da ya rataya a wuyan gwamnatin kasar Sin, kuma mataki ne da ya dace, kana yake bisa turba.

Ya ce babu wani daga waje dake da ikon tsoma baki cikin harkokin kasar Sin, bare ma ya yi yunkurin amfani da batun HK wajen yi wa kwanciyar hankalin kasar zagon kasa.

Bugu da kari, ya ce Mali na adawa da yi wa harkokin cikin gidan Sin katsalandan, kuma tana matukar goyon bayan kokarin Sin din, na kare tsaro da cikakken ikonta. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China