Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jirgin saman kasar Sin samfurin AG600 mai iya tashi da sauka akan ruwa da kasa, ya yi tashinsa na farko daga teku
2020-07-27 11:19:33        cri

Jirgin saman AG600, kirar kasar Sin dake iya sauka da tashi kan ruwa da kuma kasa, ya yi nasarar tashi na farko daga kan teku, da safiyar jiya Lahadi a Qingdao dake lardin Shandong na gabashin kasar.

Kamfanin kera jiragen sama mallakar gwamnatin kasar Sin na AVIC, ya ce nasarar tashin jirgin daga kan teku, wani mataki ne na ci gaba wajen kera jirgin, bayan tashinsa na farko a shekarar 2017, da kuma dagawa da kan ruwa da ya yi a karon farko daga mattatarar ruwa, a shekarar 2018.

Jirgin na AG600 tare da samfurin Y-20 mai dakon kayayyaki da samfurin C919 mai jigilar fasinjoji, wani bangare ne, na muhimmin aikin kasar Sin na samar da jiragen sama bisa dogaro da kanta.

Jirgin AG600 da aka yi wa lakabi da Kunlong, wani muhimmin jirgi ne ga tsarin aikin ceton gaggawa na kasar Sin.

An tsara jirgin ne ta yadda zai cimma bukatun kasar a fannin yaki da gobarar daji da ceto cikin ruwa da sauran ayyukan ceto na gaggawa.

Bisa tsarin ayyukansa, jirgin na iya zirga-zirga tsakanin wurin da ake gobara da wajen samar da ruwa, inda a kowacce tafiya, zai iya daukar ruwa ton 12 tare da zuba shi a wuri mai fadin murabba'in mita 4,000.

An kuma tsara shi ne ta yadda zai iya jure yanayi da muhalli mai tsanani. Yayin ayyukan ceto, zai iya gudanar da bincike a saman ruwa tare da jagorantar ayyukan ceto cikin ruwa. Yana kuma iya ceton mutane 50 yayin kowanne aiki.

Kamfanin AVIC ya ce zai ci gaba da aikin kera jirgin samfurin AG600, inda masu kerawa za su mayar da hankali kan irin jirgin mai ceto yayin gobara, wanda ake sa ran kammalawa a shekarar 2023. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China