Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta taimakawa jam'iyyar NNP mai mulkin Ghana da kayayyakin yaki da COVID-19
2020-07-28 09:59:30        cri

Sashen kula da harkokin kasa da kasa na kwamitin koli na JKS, a jiya Litinin ya mikawa jam'iyyar NPP mai mulkin kasar Ghana kayayyakin yaki da cutar COVID-19.

Kayayyakin sun hada da bandura 6,000 na kyallen rufe baki da hanci da likitoci ke amfani da shi, don taimakawa jam'iyyar hada yaduwar cutar tsakanin mambobinta.

A jawabinsa yayin bikin mika kayayyakin, jami'in diflomasiya a ofishin jakadancin kasar Sin dake Ghana Zhu Jing, ya bayyana kudirin JKS na ganin al'ummar Ghana sun magance duk wani kalubale, a wannan lokaci da jama'ar Ghana ke fama da wahalhalu

Ya kara da cewa, sashen harkokin kasa da kasa na kwamitin koli na JKS, ya baiwa jam'iyyar NPP wadannan kayayyaki ne, domin taimaka mata hana yaduwar annobar tsakanin mambobi da jami'an jam'iyyar.

Da yake karbar kayayyakin, shugaban jam'iyyar NPP Frederick Armah Blay, ya bayyana godiya ga gwamnatin kasar Sin da JKS kan yadda suke ci gaba da taimakawa kasar Ghana. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China