Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Kenya ya bullo da sabbin matakan yaki da COVID-19
2020-07-28 10:33:47        cri

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, a jiya Litinin ya bullo da wasu sabbin matakan hana yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, ganin yadda a cikin makonni uku da suka gabata, cutar ke ci gaba da yaduwa cikin sauri a wasu sassan kasar.

Kenyatta wanda ya bayyana haka yayin da yake yiwa 'yan kasar jawabi, bayan da gwamnoni 47 na kasar suka haramta sayar da barasa a dakunan cin abinci a fadin kasar, baya ga rufe dukkan mashaya, don rage yaduwar cutar a fadin kasar.

Haka kuma shugaban ya tsawaita dokar hana fita da aka sanya a fadin kasar na wasu Karin kwanaki 30, inda ya umarci 'yan sanda, da su tabbatar da ganin ana aiwatar da dokokin da ma'aikatar lafiya ta gindaya game da taruwar jama'a, musamman yadda ake binne wadanda suka mutu sanadiyar cutar

Shugaban ya ce, ma'aikatar lafiya za ta fito da wani tsari, ta yadda za a dawo da ma'aikatan da suka kware a fannin ba da maganin hana jin radadin tiyata da sashen gobe da nisa da suka yi ritaya, don taimakawa ma'aikatan lafiya dake kula da wadanda suka kamu da COVID-19 dake cikin matsanancin hali.

Ya ce, ya kamata duk kan hukomomin gwamnati, ciki har da cibiyoyin wasanni, da makarantu da sauran gine-ginen gwmnati, wadanda sakataren lafiya ya ayyana su a matsayin cibiyoyin kula da lafiyar jama'a, a mika su ga ma'aikatar lafiyar kasar, inda za a rika killacewa da kuma kwantar da wadanda suka kamu da cutar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China