Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masani: Bankin AIIB yana baiwa kasashen Afirka damar samun jari
2020-07-31 09:42:01        cri
Mai baiwa kungiyar tarayyar Afirka (AU) da hukumar MDD mai kula da harkokin tattalin arzikin Afirka(EAC) shawara kan harkokin tattalin arziki, Costantinos Bt.Constantinos ya bayyana cewa, bankin zuba jarin samar da ababan more rayuwa na Asiya(AIIB) yana baiwa kasashen Afirka damar samun kudaden jari da kwarewa a fannin samar da ababan more rayuwa.

A zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin, masanin ya ce, a matsayinsa na hukumar kula da harkokin kudi da kasashe da dama suka kafa, da ya himmatu wajen samar da rancen kudade, bankin ya baiwa kasashe da dama na Afirka dama ta cin gajiyar rance da kwarewa a bangaren samar da ababan more rayuwa.

A cewar masanin, kasashe da 'yan kasuwan Afirka, su kan fuskanci gibi a fannin samun rance, a kokarin da suke na gamsar da masu zuba jari na cikin gida da ketare, da sauran al'ummomin 'yan kasuwa game da wasu manufofi da suke fatan cimmawa.

Ya ce, a halin yanzu mambobin bankin,sun samar da gamsansun shaidu game da alkiblar manufofin gwamnatin kasashensu.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China