Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojoji mata na Sin suna nuna kwazo wajen shimfida zaman lafiya a Mali
2020-08-01 16:52:36        cri

Hausawa kan ce, kallabi tsakanin rawuna. Akwai sojoji mata na kasar Sin da dama, wadanda suke nuna himma da kwazo wajen kiyaye zaman lafiya a kasar Mali. Bayan jibge su a watan Mayun bara a Mali, sojoji mata 14 masu aikin jinya kashi na 7 da kasar Sin ta tura suna gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya daban-daban cikin nasara, duk da cewa suna fuskantar barazanar hare-haren ta'addanci da annobar COVID-19.

Kawo yanzu, wadannan sojoji masu aikin jinya na kasar Sin sun duba marasa lafiya da yawansu ya kai 2,944, da gudanar da ayyukan tiyata har sau 58. Bayan barkewar cutar COVID-19 a wurin da suke gudanar da aikin shimfida zaman lafiya a Mali, asibitin da sojojin Sin suka kafa ya zama asibiti daya kacal na tawagar shirin MINUSMA na MDD mai wanzar da zaman lafiya a Mali, wanda ke iya ci gaba da gudanar da ayyukan samar da magani ga marasa lafiya, al'amarin da ya shaida cewa, sojojin kasar Sin sojoji ne wadanda suka cancanci amincewa, har ma sun samu lambar karramawa daga tawagar ta MINUSMA saboda jajircewar da suka yi na ceton rayuka a wuraren da ake kiyaye zaman lafiya.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China