Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan Boko Haram sun kashe fararen hula 18 a yankin Far North na Kamaru
2020-08-03 09:35:18        cri
A kalla fararen hula 18 aka kashe a wani hari dake da alaka da mayakan kungiyar Boko Haram a daren Asabar zuwa wayewar garin Lahadi a yankin Far North na jamhuriyar Kamaru, wata majiya daga yankin ta tabbatar da lamarin.

An kaddamar da harin ne a wani waje da ake kira Nguetchewe, a shiyyar Mayo-Moskota dake kusa da kan iyakar Najeriya, inda mayakan Boko Haram ke cin karensu babu babbaka. An kuma yiwa wasu kauyawa 11 munanan raunuka, kamar yadda wata majiya da ta nemi a sakaye sunanta ta tabbatar.

Wannan harin ya zo ne kimanin makonni biyu bayan kashe sojoji da mayakan Boko Haram suka yi a garin Touski dake yankin Far North, bayan kashe wasu 'yan Najeriya a yankin Kordo wanda mayaka masu ikirarin jihadi suka yi, har yanzu wannan yankin na jamhuriyar Kamaru yana fama da tabarbarewar tsaro tun daga shekarar 2014. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China