Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sassa daban daban na Hong Kong suna fatan ma'aikatan jinya na Guangdong za su taimaka wa yankin yaki da annobar COVID-19
2020-08-03 14:29:12        cri

Kwanan baya, yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin na fuskantar babban matsin lamba wajen dakile da kandagarkin annobar cutar numfashi ta COVID-19. Ya zuwa ranar 2 ga wata, kwanaki 12 a jere ke nan ana samun sabbin masu kamuwa da annobar fiye da 100 a ko wace rana. A kokarin biyan bukatun mahukuntan Hong Kong, gwamnatin tsakiyar kasar Sin ta tura ma'aikatan jinya zuwa yankin don gudanar da ayyukan gwajin cutar, da taimakawa mahukuntan yankin yaki da annobar. Sassa daban daban na Hong Kong suna ganin cewa, ma'aikatan jinya daga babban yankin kasar Sin sun kware wajen yaki da annobar, za kuma su taimaka wa Hong Kong cike gibin da ke akwai a wannan fanni.

Kwararru 7 kan gwajin COVID-19, sun isa Hong Kong daga babban yankin kasar Sin da yammacin jiya Lahadi, a matsayin kashin farko na ayarin da za su taimaka wajen dakile bazuwar COVID-19 dake kara kamari a yankin. Kwararrun, wadanda za su taimaka da ayyukan gwaje-gwaje, mambobi ne na ayarin kwarraru 60 masu gwajin COVID-19 da hukumar kiwon lafiyar lardin Guangdong ta zaba daga asibitoci fiye da 20 a lardin a kwanan nan. Kwararrun 7 sun samu maraba da hannu bibbiyu a otel din da suka kwana a Hong Kong. Nan gaba ayarin zai taimaka da kara gudanar da gwaje-gwajen COVID-19 a tsakanin al'ummar Hong Kong, bisa taimakon hukumomin yankin masu ruwa da tsaki. Dangane da lamarin, Wu Zhibin, mai ba da shawara ga hukumar darektoci na asibitin Yan Chai na Hong Kong ya ce,"Ma'aikatan lafiya na kasarmu sun kware wajen yaki da annobar COVID-19. Gwajin annobar a Hong Kong yana da matukar muhimmanci wajen toshe hanyoyin yaduwarta baki daya. Amma Hong Kong bai iya cike gibin da ke akwai ba tukuna. Na ji an ce, yanzu mutane dubu 8 zuwa dubu 9 ne kawai ake musu gwajin annobar a ko wace rana, hakan bai biyan bukatun yankin ba. Haka kuma ba mu da isassun dakunan jinyar masu kamuwa da cutar. Ma'aikatan jinya daga babban yankin kasarmu sun biya bukatunmu kwarai da gaske, sun taimaka mana wajen kyautata abubuwan da muka gaza yi."

Kwararru daga masana kimiyya da fasaha ta fuskar likitanci a Hong Kong sun yi nuni da cewa, kungiyoyin masu gwajin annobar da kuma kunyoyin taimakawa asibitocin wucin gadi da kwamitin kiwon lafiya na kasar Sin ya kafa cikin gajeren lokaci, za su ba da tallafi wajen tsara fasalin asibitoci, tafiyar da su da sauran ayyuka masu ruwa da tsaki, lamarin da zai taimakawa ma'aikatan jinyar Hong Kong sosai. Guan Qiaozhong, shugaban kamfanin kimiyya da fasahar halittu na Kaipu ya bayyana cewa, "Yanzu kasarmu ta kasance a matsayi na farko a duniya wajen gwajin annobar ta COVID-19. Kamfaninmu da takwarorinmu sun fito da wasu kayayyaki masu inganci. Kara yin gwaje-gwajen COVID-19 a Hong Kong da kuma samun nagartattun hanyoyi da dabarun jinyar masu kamuwa da cutar za su taimaka wa ma'aikatan jinyar Hong Kong sosai."

Har ila yau, sassa daban daban na Hong Kong suna ganin cewa, yayin da annobar ta COVID-19 ta kara yin kamari a yankin, ma'aikatan gwajin annobar sun isa yankin cikin gajeren lokaci, hakan ya nuna kulawa da goyon baya daga al'ummar babban yankin kasar Sin, zai kuma daidaita matsalolin karancin isassun albarkatun kiwon lafiya da ma'aikatan jinya a Hong Kong. Madam Tang Anying, wadda ta kafa kawancen 'yan kasuwan lardin Sichuan a Hong Kong ta ce,"Wadannan kwararrun da suka shirya zuwa Hong Kong, kwararru ne da gwamnatin tsakiyar kasarmu ta tura zuwa yankin domin taimakawa yaki da annobar. Sun jure wahala a farkon lokacin barkewar annobar. Sun kware wajen kandagarki da dakile annobar. A cikin kwanaki 10 kadai aka kammala gwajin annobar kan mutane fiye da miliyan 9 a birnin Wuhan. Ba za a gamu da wata matsala ba a yankin na Hong Kong, inda ake da mutane fiye da miliyan 7. Tabbas za su taimaka wajen gwajin annobar kan dukkan al'ummar yankin, da warware matsalar karancin isassun albarkatu da ma'aikatan lafiya a yankin." (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China