Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hukumar FAO ta yi gargadin farin dango ka iya kaura daga gabashin Afrika zuwa yammaci
2020-08-03 14:20:33        cri
Hukumar samar da abinci da kula da aikin gona ta MDD, ta yi gargadi a jiya cewa, adadi mai yawa na farin dango dake a yankin kahon Afrika, galibi a kasashen Habasha da Kenya tun cikin watan Janairun bana, ka iya kaura zuwa yankin yammacin nahiyar cikin makonni masu zuwa, inda suke barazana ga gonaki da makiyaya da rayuwar jama'a a yammacin Africa.

Hukumar wadda ta yi gargadi game da farin, ta jaddada cikin rahotonta na baya-bayan nan cewa, ana gudanar da aikin sa ido a kasashe yadda ya kamata, sannan an shirya matakan dakile farin saboda samun gargadin wuri da aka samu da kuma matakan tunkararsu da FAO din ta tsara.

Sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce an fuskanci barazanar da ba a taba gani ba kan wadatar abinci da rayuwar jama'a a gabashin Afrika, kuma ana yin dukkan mai yuwuwa wajen kare aukuwar makamanciyar matsalar a yankin Sahel, wanda a yanzu haka ke fuskantar matsaloli da dama. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China