Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutuwar da aka samu a sanadiyyar COVID-19 a Afrika ya doshi 20,000 mutane 944,450 sun kamu da cutar
2020-08-03 15:49:26        cri
Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Afrika CDC ta ce adadin mace macen da aka samu a nahiyar Afrika sanadiyyar cutar numfashi ta COVID-19 ya kai 19,920, yayin da mutanen da aka tabbatar sun harbu da cutar ta ya kai 944,450 ya zuwa ranar Lahadi.

Africa CDC, kwararriyar hukumar lafiya ta kungiyar tarayyar Afrika AU, ta bayyana cikin sabbin alkaluman da ta fitar a ranar Lahadi cewa, adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a fadin nahiyar ya karu daga 927,661 a ranar Asabar zuwa 944,450 a ranar Lahadi.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China