Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan masu COVID-19 a Afrika ya kusa kaiwa miliyan 1 yayin da ake kira da a gaggauta dakile ci gaba da yaduwar cutar
2020-08-07 10:51:57        cri

Cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta Africa CDC, ta ce adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da annobar COVID-19 a fadin nahiyar ya kai 992,710.

Afrika ta Kudu, ita ce kasar da ta fi kowacce yawan masu cutar a nahiyar, inda ta bada rahoton mutane 521,318 da suka kamu da cutar, sai kasashen Masar da Nijeriya da Morocco dake bi mata baya.

Baya ga yaduwar da cutar take cikin sauri a fadin nahiyar, cibiyar Afrika CDC ta ce wasu kasashen nahiyar 8 sun bada rahoton adadin wadanda cutar ta yi ajalinsu da ya dara matsakaicin matakin na duniya baki daya.

A cewar cibiyar, kasashen da aka fi samun wadanda suka mutu sun hada da Chadi da wadda ke da kimanin kaso 8 sai Sudan da Niger da Liberia da kaso 6 kowannensu, sai Masar da Mali da Burkina Faso da Angola da kaso 5 kowanne.

Ta kuma yi gargadin cewa wasu kasashen Afrika kalilan ne ke bada rahoton adadi mafi yawa na masu cutar.

A cewarta, daga ranar 28 na watan Yuli, kasashen Afrika 6 sun bada rahoton kimanin kaso 80 na sabbin mutanen da suka kamu da cutar, inda suka hada da Afrika ta Kudu mai kaso 58 sai Morocco mai kaso 5 da Algeria da Kenya da Ghana da Habasha da kaso 4 kowanne, na jimilar sabbin wadanda suka kamu a makon da ya gabata.

Yayin da cutar ke kara yaduwa a nahiyar, Afrika ta Kudu da Djibouti da Sao Tome and Principe da Cape Verde da Gabon, sun fi bada rahoton wadanda suka kamu.

Hukumar AU ta yi gargadin cewa, tasirin yaduwar cutar a Afrika ka iya dadewa kamar yadda yaduwarta ya yi, baya ga matakan kulle da aka kakaba a nahiyar da ka iya illata tsarin zaman takewa da tattalin arziki da kiwon lafiya masu rauni a nahiyar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China