Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin mutanen da cutar COVID-19 ta harba a Afrika ya zarce miliyan guda sannan ta kashe mutane 22,491
2020-08-09 15:40:29        cri
Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Afrika CDC ta sanar a ranar Asabar cewa, adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a nahiyar Afrika ya kai 1,022,084.

Africa CDC, kwararriyar hukumar lafiya ta kungiyar tarayyar Afrika AU, mai mambobin kasashe 55, cikin alkaluma na baya bayan nan da ta fitar a ranar Asabar ta ce, adadin mutuwar da aka samu masu nasaba da cutar COVID-19 ya karu daga 22,066 a ranar Juma'a, zuwa 22,461 a ranar Asabar.

Cibiyar dakile cutuka ta nahiyar ta kara da cewa, adadin mutanen da suka warke daga cutar COVID-19 a Afrika ya zarce 700,000.

A bisa ga alkaluman kididdigar da Africa CDC ta fitar, majinyata 705,016 ne suka warke daga annobar COVID-19 a fadin nahiyar Afrika ya zuwa ranar Asabar, wato an samu karin sabbin mutane 14,580 da suka warke daga cutar a ranar Asabar.

Afrika ta kudu ce kasar da ta fi yawan masu dauke da cutar a nahiyar, sai kasashen Masar, Najeriya, Algeria da Morocco, dake bi mata baya. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China