Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnonin Najeriya sun bukaci a samarwa sojoji kayan yaki na zamani a shiyyar arewa maso gabashin kasar
2020-08-10 10:28:55        cri

Gwamnonin jahohi a Najeriya sun bukaci gwamnatin tarayyar kasar da ta tura karin sojoji da kayan yaki na zamani dake yaki da mayakan Boko Haram a shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Babagana Zulum, shugaban kungiyar gwamnonin arewa maso gabashin Najeriya, kana gwamnan jahar Borno, shi ne yayi wannan kira cikin wata sanarwa da aka baiwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a ranar Lahadi, bayan kammala taro na biyu na kungiyar gwamnonin domin tattauna kalubalolin tsaro dake addabar shiyyar wanda suka gudanar a ranar Asabar.

Kiran na gwamnonin jahohin Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba, da jahar Yobe, ya zo ne makonni kadan bayan 'yan bindiga sun kaddamar da hari kan ayarin gwamna Zulum a yankin Baga dake jahar Borno.

Gwamnonin sun yabawa kokarin da gwamnatin tarayyar kasar ke yi a yaki da 'yan tada kayar baya, inda suka bukaci sojojin kasar da su kara azama wajen kutsawa lungu da sako domin tabbatar da tsaro don manoma su samu damar komawa gonakinsu.

Sanarwar ta ce, kungiyar gwamnonin ta bayar da shawarar a yi kokarin cike gibin da ake da shi a rundunar sojojin kasar ta hanyar baiwa 'yan sanda makamai da sauran muhimman kayayyakin aiki da suka dace kamar hayaki mai sa hawaye mai tsananin zafi, da na'urar na'urar bin sawun mutane da motoci masu sulke.

Haka zalika sun bukaci sojoji su dauki kwararan matakai domin kawo karshen ayyukan 'yan ta'adda, domin baiwa mutanen da rikici ya daidaita damar sake komawa garuruwansu. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China