Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin WHO: Kwayar cutar COVID-19 ba ta sauya sakamakon sauyin yanayi ba
2020-08-11 13:13:54        cri

A jiya Litinin 10 ga wata, masanin hukumar lafiya ta duniya wato WHO ya bayyana cewa, kawo yanzu kwayar cutar numfashi ta COVID-19 ba ta sauya sakamakon sauyin yanayi ba, amma idan ba a ci gaba da daukan tsauraran matakan kandagarkin cutar ba, to, za ta sake barkewa a ko da yaushe.

A cikin 'yan kwanakin da suka gabata, adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19 ya karu a wasu kasashen Turai wadanda suka riga suka samu sakamako a bayyane wajen hana yaduwar annobar, inda kafofin watsa labarai sun gabatar da rahotanni cewa, kasashen Turai suna fuskantar barazanar sake barkewar annobar.

A jiya Litinin, jagoran aikin gaggawa na hukumar lafiya ta duniya wato WHO Michael Ryan ya bayyana a yayin taron hukumar game da yanayin da ake ciki na dakile annobar COVID-19 cewa, akwai yiyuwar sake barkewar annobar, a don haka ya dace kasashen dake yankin yammancin Turai su kara mai da hankali kan yaduwar cutar ta hanyar taruwar mutane ko a cikin unguwanni, tare kuma da aiwatar da matakan kandagarkin annobar da suka dace da yanayin da suke ciki, ta yadda za a gujewa sake daukan matakan kulle a fadin kasar.  Ya ce, "Kawo yanzu, kwayar cutar COVID-19 ba ta sauya sakamakon sauyin yanayi ba, amma an lura cewa, idan ba a ci gaba da daukan tsauraran matakan kandagarkin annobar ba, tabbas kwayar cutar za ta yadu cikin sauri, idan kuma har hakan ya faru, ana iya kiran lamarin sake barkewar annobar."

A yayin taron hukumar game da yanayin dakile annobar da ake ciki da aka kira jiya, babban darektan hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya furta cewa, a cikin watanni uku da suka wuce, hukumar ta gabatar da shiri mai taken "hanzarta samun maganin ganin bayan annobar COVID-19" ta hanyar gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, yanzu haka, an riga an fara mataki na biyu ko uku na gwajin allurar riga kafin cutar, kuma gwaje-gwajen sun samu halartar kasashe sama da 160 a fadin duniya. A sa'i daya kuma, an fara yin amfani da wasu magunguna da aka yi amfani da su yayin jinyar masu cutar wadanda ke cikin yanayi mai tsanani, kana likitocin suna nazarin sabbin dabarun jinya.

Babban darektan ya kara da cewa, a cikin watanni uku masu zuwa, za a kara ingiza shirin samun maganin ganin bayan annobar COVID-19, domin taimakawa wajen dakile annobar a fadin duniya, amma abun takaici shi ne, ana fama da karancin kudin gudanar da aikin, yana mai cewa, "Duk da cewa, shirinmu na hanzartar samun maganin ganin bayan annobar COVID-19 yana da ma'ana matuka, amma muna fama da karancin kudi, zai yi wahala mu samu isasshen kudin gudanar da aikin, saboda muna bukatar dala sama da biliyan daya, amma yanzu mun samu dala miliyan 100 ne kawai."

Kana babban darektan ya jaddada cewa, a halin da ake ciki yanzu, duk da cewa, ana fuskantar yanayi mai tsanani a bangaren hana yaduwar annobar, amma idan shugabannin kasashen duniya suka dauki tsauraran matakan kandagarkin cutar, haka kuma al'ummun kasashen suka amince da matakan, akwai yiyuwar hanzarta hana yaduwar annobar, alal misali a makon jiya, kasar New Zealand ta sanar da cewa, ba a samu rahoton sabbin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a cikin kwanaki 100 da suka gabata ba, kuma kasar Ruwanda dake nahiyar Afirka ita ma ta samu sakamako mai kyau wajen kandagarkin cutar, yana mai cewa, "A cikin makon da muke ciki, adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a fadin duniya zai kai miliyam 20, kuma adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar zai kai dubu 750, wadannan adadi babbar masifa ce, ko kuma abin bakin ciki ne, saboda rayuka suna da daraja matuka, na san kowa da kowa dake wurare daban daban a fadin duniya suna cikin bacin rai, a don haka ina faran za a kara kokari domin gaggauta hana yaduwar cutar"(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China