Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zimbabwe ta yi bikin cika shekaru 40 da tuna 'yan mazan jiya
2020-08-11 11:38:03        cri
Jiya Litinin ne, kasar Zimbabwe ta yi bikin cika shekaru 40 da tunawa da 'yan mazan jiya, a yayin da cutar COVID-19 ke yaduwa a kasar.

A jawabin da ya gabatar ta kafar talabijin yayin bikin da aka gudanar ba tare da shagugulan da aka saba shiryawa ba, shugaba Emmerson Mnangagwa ya bayyana cewa, bikin na da muhimmanci a tarihi da ma ci gaban kasar, a yayin da take martaba 'yan mazan jiya da suka sadaukar da rayukansu wajen 'yantar da kasar daga Turawan mulkin mallakar Burtaniya.

Shugaban Mnangagwa ya ce, an gudanar da bikin na wannan shekara, yayin da ake yaki da makiya kasar a ciki da wajen kasar. Ya kuma lashi takwabin cewa, karyar rarrabuwar kawuna da masu sukar lamarin duk wani tsari gami da masu nuna fifiko kan wasu, dake neman kwace albartun kasar, ba za su yi nasara ba.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China