2020-08-11 12:06:47 cri |
Rene Van Dongen, wakilin hukumar UNICEF a Tanzania ya ce, takardar shaidar haihuwa wata muhimmiyar takarda ce dake tabbatar da haihuwar yaro.
Jami'in na UNICEF ya bayyana haka ne a lokacin kaddamar da sabon tsarin saukaka yin rajistar haihuwar yara a shiyyoyin Tanga da Kilimanjaro, inda ake sa ran yi wa yara 'yan kasa da shekaru biyar sama da dubu 580 rajistar haihuwar nan da watanni biyu masu zuwa.
Tanga da Kilimanjaro, sun shiga sahun shiyyoyin kasar 16 inda aka yiwa yara 'yan kasa da shekaru biyar sama da miliyan 4.6 rajistar haihuwar tun bayan kaddamar da shirin a shekarar 2013.
Sabon tsarin ya haifar da samun karuwar rajistar haihuwa ga yara 'yan kasa da shekaru biyar a wadannan shiyyoyi na kasar daga kasa da kashi 10 bisa 100 zuwa sama da kashi 80 bisa 100.
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China